Kungiyar Hamas ta ce hare-haren da yahudawa ‘yan mamaya suka kai a makarantar Mustafa Hafez da ke yammacin birnin Gaza, wani lamari ne da ke tabbatar da irin zubar da jinin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da aikatawa.
Falasdinawa 12 ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace a karkashin baraguzan gine-gine, yayin da wasu da dama suka jikkata, lokacin da sojojin mamaya suka kai hari a makarantar Mustafa Hafez, da ke dauke da mutane 700 dake zaman mafaka, a ranar Talata, a cewar bayanan da jami’an tsaron farar hula na Gaza suka fitar.
Hamas ta dora alhakin duk laifukan da Isra’ila ke aikatawa ga shugaban Amurka Joe Biden da gwamnatinsa.
‘’Duk wadanan laifuka suna ci gaba ne tare da goyan bayan Amurka ta fuskar siyasa da soja da suke baiwa gwamnatin sahyoniya’’ inji Hamas.
Kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da cibiyoyinta da su yi aiki tukuru domin kawo karshen wadannan laifuffuka da cin zarafi da ake yi wa fararen hula da ba su dauke da makamai.
Ta kuma yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta tattara bayanan kisan gillar da aka yi, ta kuma fara hukunta shugabannin mamaya kan wadannan laifuffukan da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, a cewar Hamas.
Bayanai da hukumar tsaron fararen hula a zirin Gaza ta fitar, sun ce sojojin mamaya sun yi ruwan bama-bamai kan makarantu 9 da ke dauke da daruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu a zirin Gaza a cikin watan Agusta.