Hamas Ta Dauki Alhakin Kai Harin Da Ya Kashe ‘Yan Isra’ila 7

Hamas ta ce mayaƙanta ne suka kashe mutum bakwai a Tel Aviv Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ita ce ta kai harin bindiga

Hamas ta ce mayaƙanta ne suka kashe mutum bakwai a Tel Aviv

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ita ce ta kai harin bindiga da na wuka a Tel Aviv a ranar Talata, inda aka kashe mutum bakwai.

Hamas ta ce maharan mayakanta ne daga birnin Hebron a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Lamarin ya faru ne kusa da tashar jirgin kisa a yankin Jaffa na Tel Aviv.

Hamas dai na hare-haren ramuwar gayya kan yakin kisan kare dangin da Isra’ila ta shelanta kan Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 364 ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,638.

A Isra’ila kuwa mutum 1,928 ne suka mutu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments