Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa hare-haren da HKI ta kai shuwagabannin kungiyar masu tattaunawa a doha a ranar talatan da ta gabata, ba zai sauya

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa hare-haren da HKI ta kai shuwagabannin kungiyar masu tattaunawa a doha a ranar talatan da ta gabata, ba zai sauya kome a abinda kungiyar zata gabatar na sulhu a Gaza ba. Shafin yanar gizo na labarai “Arab News” ya nakalto Fawzi Barhoum yana fadar haka a wani faifen bidiyo da aka watsa a kafafen yada labarai a yau Alhamis.

Hamas ta bayyana cewa tana da tabbaci kan cewa gwamnatin kasar Amurka, ko kuma shugaba Trump yana da hannu a cikin wannan makircin na kokarin kashe shuwagabannin Hamas a Doha.

A ranar talata ce HKI ta yi kokarin kashe tawagar tattaunawar sulhu da kuma zaman Lafiya na kungiyar Hamas a binin Doho wanda bai sami nasara ba, amma gwamnatin Amurka ta yi kokarin nunawa gwamnatin kasar Qatar da kuma duniya kan cewa HKI ce ta shiya ta kuma aiwatar, don haka gwamnatinsa bata da hannu, sannan ba bawa gwamnatin Qatar hakuri tare da alkawalin cewa hakan ba zai faruba.  Barhoum ya kara da cewa wannan kokarin kissan ya kashe dukkan wani shiri na samar da zaman lafiya a gaza.

Natanyahu dai yana neman a samar da wata sabuwar yarjeniya wacce zata fito da dukkan fursinonin yakin yahudawa da suke hannun kungiyar Hamas, wanda kuma karfi ya kasa fito da su daga hannun ita Hamas. A halin yanzu dai akwai fursinonin yahudawa kimani 59 a hannun kungiyar Hamas. Wasu daga cikinsu sun mutu sai dai a bada gawakinsu. Dukkan shuwagabannin Hamas 5 da suke tattaunawar sun tsira da rayukansu bayan harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments