Bangaren soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya ce a shirye yake kan komi ma, kuma zai ci gaba da kasancewa cikin “kyakyawan shiri”, yana mai jaddada cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake yaki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ba zai sa a sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su ba.
Abu Ubaida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a faifan bidiyo a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa, abin da ‘yan mamaya suka kasa cimma ta hanyar “makamai da yaki” ba za a taba samun shi ba ta hanyar “barazana da yaudara ba.”
Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa za a kashe Falasdinawa a zirin Gaza da mayakan Hamas matukar ba’a gaggauta sako sauran Isra’ilawan da ke hannun Hamas ba.
Shugaba Trump ya bukaci Hamas ta gaggauta sakin dukkan mutanen da take garkuwa da su a Gaza – inda ya yi barazanar cewa za ta dandana kudarta idan har ba ta saki sauran mutanen ba.
Ya kuma yi kira ga Hamas ta fice daga yankunan Falasdinawa tare da yin gargadi ga al’ummar Gaza cewa za su fuskanci mutuwa idan har ba a saki mutanen da Hamas ke tsare da su ba.
Trump ya yi gargadin ne ga Hamas a sakon da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta inda ya ce zai sa Isra’ila ta kammala aikin da ta soma wajen kakkabe Hamas.
Gargadin na Trump na zuwa ne yayin da Fadar White House ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da Hamas domin sakin mutanen da kungiyar ke tsare da su.