Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da azabtarwar da Isra’ila take yi wa Falasdinawa da take tsare da su a gidan yarin Megiddo, tare da yin kira ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa da ta rubuta irin wadannan laifuka a cikin jerin laifukan yaki na Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, cin zarafi da wulakanci da sojojin mamaya suka yi wa fursunonin Palasdinawa a gidan yarin na Megiddo, ya nuna irin tsananin kyama da mummuniyar yahudawa masu tsaron gidan yarin a kan falastinawa.
“Wadannan laifukan wani bangare ne na cin zarafi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi wa fursunonin Falasdinu, wadanda suka hada da azabtarwa, cin zarafi, horo da yunwa, rashin kulawa ta fuskaar lafiya da gangan, da kuma tauye hakkin dan Adam.
A kan haka, adadin Falasdinawa da suka rasa rayukansu sakamakon sakaci da azabtarwa ya zarce 60,” in ji sanarwar.
Hotunan da aka fallasa daga gidan yarin na Megiddo sun nuna yadda sojojin Isra’ila ke cin zarafin fursunonin Falasdinu tare da tsoratar da su da karnuka.
Bidiyon ya nuna fursunoni da dama kwance a kasa tare da daure hannayensu a bayan bayansu, wasu daga cikinsu ba su da tufafi, yayin da jami’an tsaron Isra’ila suke cin zarafinsu da kuma sakar musu karnuka masu cizo.
A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa da suka hada da (ICRC) da su rubuta irin wannan cin zarafi da sauran munanan laifuka kan fursunonin Palasdinawa.
Har ila yau, ta bukaci hukumomin duniya da su dauki matakin gaggawa don matsa lamba kan Isra’ila da Benjamin Netanyahu, kan su daina keta dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin fursunoni, da kuma dorawa shugabannin Isra’ila alhakin ci gaba da laifukan da suke yi.