Hamas ta bayyana muhimman bukatunta a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana manyan sharudan ta a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta bayyana cewa tana kokarin shawo kan

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana manyan sharudan ta a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta bayyana cewa tana kokarin shawo kan duk wani cikas domin cimma yarjejeniyar da ta dace da muradun al’ummar zirin Gaza.

Kakakin kungiyar Fawzi Barhoum ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa a Masar kan shirin tsagaita bude wuta da shugaban Amurka ya gabatar da nufin kawo karshen yakin Gaza.

Ya bayyana cewa, bukatun Hamas sun hada da tsagaita bude wuta na dindindin, da janyewar Isra’ila gaba daya daga Gaza, da shigar da kayayyakin jin kai da na agaji ba tare da sharadi ba, da mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu, da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni ta gaskiya.

M. Barhoum ya zargi fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da neman dakile zagayen tattaunawar da ake yi a halin yanzu, kamar yadda ya yi a baya.

A ranar 6 ga watan Oktoba ne tawagogin Isra’ila da Hamas suka fara tattaunawa a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh a Masar kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na Gaza.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan shirin Trump na Gaza mai daftarori guda 20, shirin da gwamnatin Tel Aviv ta amince yayin da ita kuma Hamas ta amince da wani bangare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments