Hassam Badron wani mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar Hamas a nan Tehran ya bayyana cewa babu wani jami’an kungiyar a taron da ke gudana a halin yanzu a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da musayar Fursinoni da HKI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Tashar Talabijin ta Falsdin ta nakalto Hassam Badron yana cewa babu wani jami’an kungiyar Hamas a alkahira, ba don kome ba saboda sharuddan da gwamnatin HKI ta shimfida na tsagaita wuta bai sami amincewar mutanen gaza ba.
Labarin ya kara da cewa tuni tawagar HKI ta isa birnin Alkahira don tattauna kan batun tsagaita wuta a gaza da kuma musayar fursinoni.
Har’ila yau Hassan ya kara da cewa shawarar mika harkokin gudanarwa zirin gaza ga wata hukuma ta kasa da kasa ba abinda amincewa bani ga mutanen gaza, don ba zasu amince da a dora masu wasu mutanen daga waje don gudanar da ayyukar shugabanci a yankin gaza ba