Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta.
Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.”
Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken.
Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare.
Na baya bayan su ne ta jirgin sama mara matuki a kusa da garin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kashe akalla mutane biyu, a cewar majiyoyin lafiya.
Masu ba da agajin gaggawa a Asibitin Nasser sun ba da rahoton cewa wani jirgin sama mara matuki na Isra’ila ya kai hari kan wasu a garin Abasan al-Kabira a ranar Litinin.
Tun bayan fara yakin kare dangi na Isra’ila a watan Oktoba na 2023, gwamnatin mamaye ta kashe akalla Falasdinawa 68,527 galibi mata da yara.