Search
Close this search box.

Hamas : Netanyahu Da Biden Ne Silan Kisan Da Akayi Wa Wadanda Ake Garkuwa Dasu

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta dora alhakin kisan da aka yi wa mutum shida daga cikin wadanda akayi Garkuwa dasu a Gaza a kan

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta dora alhakin kisan da aka yi wa mutum shida daga cikin wadanda akayi Garkuwa dasu a Gaza a kan firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Joe Biden.

A cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Lahadi, Izzat al-Rishq, babban jami’in ofishin siyasa na Hamas, ya tabbatar da cewa ci gaba da ayyukan soji da gwamnatin Isra’ila ke yi da kin amincewa da tsagaita bude wuta ne ke da alhakin asarar rayukan da aka samu a tsakanin wadanda akayi garkuwa dasu.

Ya kuma zargi gwamnatin Amurka da hannu a cikin lamarin, yana mai nuni da goyon bayanta ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Al-Rishq ya ce “Alhakin mutuwar wadannan mutanen ya rataya ne a kan gwamnatin Netanyahu, wacce ke ci gaba da yakin neman zabenta na kisan kiyashi, kuma ta kaucewa tattaunawar tsagaita bude wuta, da kuma gwamnatin Amurka, wacce ke ba da tallafin kudi da soja ga gwamnatin Isra’ila.

” Ya kara da cewa, idan da gaske shugaba Biden ya damu da rayukan wadanda ake garkuwa dasu, to ya kamata ya daina duk wani goyon baya ga Isra’ila tare da matsa lamba kan dakatar da yakin.

Al-Rishq ya jaddada cewa Netanyahu, majalisar ministocinsa masu tsattsauran ra’ayi, da masu goyon bayansu na kasa da kasa za su fuskanci hukunci kan abin da ya bayyana a matsayin watanni 11 na “laifuka da kisan kare dangi” kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.

Sanarwar ta Hamas ta biyo bayan gano gawarwakin mutane shida da aka yi garkuwa da su a Rafah, kamar yadda rundunar sojin Isra’ila ta sanar a safiyar Lahadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments