Hamas : Mun Kashe Sojojin Isra’ila 10 A Gaza Cikin Sa’o’I 72

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra’ila 10 a arewacin Gaza a cikin kwanaki ukun da suka gabata. “Sama da

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra’ila 10 a arewacin Gaza a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

“Sama da sojojin Isra’ila 10 aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da ‘yan gwagwarmaya suka kai a cikin sa’o’i 72 da suka gabata,” in ji Abu Obaida, kakakin reshen Hamas, na kungiyar Qassam Brigades, a cikin wata sanarwa.

Ya ce asarar da sojojin Isra’ila suka yi “ta fi yadda aka sanar.” Ya ci gaba da cewa: “Za a yi galaba kan makiya (Isra’ila) daga arewacin Gaza.

Kakakin ya ce nasarorin da sojojin Isra’ila suka samu a arewacin Gaza su ne “lalata abubuwan more rayuwa da barna da kisan kiyashi kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.”

Tunda farko dai kafofin yada labaran yahudawan sun bayyana cewa, an kashe sojojin Isra’ila 5 tare da raunata wasu 10 a arewacin zirin Gaza a safiyar yau litinin.

Dakarun kungiyar Al-Qassam Brigade sun kai hari kan wani gini da sojojin Isra’ila suka yi amfani da shi a matsayin maboya a yankin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza.

Ma’aikatar Yakin Isra’ila ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa, wata babbar fashewa da aka yi a kusa da wani gini a yankin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza ta yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu goma, kuma 8 daga cikin wadanda suka jikkata suna cikin mawuyacin hali.

Sojojin Isra’ila sun ce an kashe sojoji kasar 840 tun farkon yakin Gaza da suka hada da 405 tun farkon mamayar kasa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments