Search
Close this search box.

Hamas: Isra’ila ce ke kawo cikas kan batun dakatar da bude wuta

Babban kusa a kungiyar Hamas Ghazi Hamad ya jaddada cewa, a halin yanzu ya zama wajibi a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauki matsaya guda.

Babban kusa a kungiyar Hamas Ghazi Hamad ya jaddada cewa, a halin yanzu ya zama wajibi a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauki matsaya guda.

Da yake magana da tashar Al Mayadeen, Hamad ya bayyana cewa Hams ta yi sassauci a kan wasu, amma firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ki yin la’akari da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, inda ya zabi ci gaba da yakin.

“Mun kalli jawabin na Biden da kyau kuma mun nuna sassauci, amma Netanyahu ya ki amincewa da shi ya zabi ci gaba da yakin,” in ji Hamad.

Ya kara da cewa, kungiyar Hamas ta yi imanin cewa Isra’ila ba ta da sha’awar cimma matsaya kan wannan batu.

Hamad ya kara da cewa da alama Netanyahu yana da niyyar ci gaba da yakin duk da matsin lamba da Isra’ila ke yi na amincewa da shawarar masu  shiga tsakani da Hamas ta amince da su. Ya kara da cewa, Netanyahu yana son ya ci gaba da kara tsunduma cikin yakin Gaza ne, ganin cewa kawo karshen yakin zai kawo karshen rayuwarsa ta siyasa, kuma zai iya tafiya gidan kaso sakamakon matsalolin da Isra’ila ta samu a lokacin mulkinsa.

“Matsayinmu a bayyane yake, yayin da har yanzu babu wani tabbaci dangane da aiwatar da abin da shawarwarin daga bangaren Isra’ila, ” in ji shi.

Ya yi nuni da cece-kucen cikin gida a cikin gwamnatin Isra’ila dangane da yarjejeniyar, yana mai cewa lamarin ya zame musu mai nauyi, inda sauye-sauyen da ake samu yankin sun sanya an farwa bijirewar mamayar Amurka da Isra’ila.

Hamad ya soki irin goyon bayan da Amurka ke baiwa “Isra’ila” ba tare da kakkautawa ba, yana mai cewa dagewar Isra’ila a kan matsayarta ta ci gaba da yaki da kisan kare dangi kan al’ummar Falastinu na tsawon shekaru masu yawa, yana da nasaba ne da goyon bayan siyasar Amurka. “Matsayinmu a bayyane yake,  kuma yana bisa ka’ida, yayin da matsalar ta ta’allaka ne ga bangaren Isra’ila da a kullum ke cewa ba za a kawo karshen yakin Gaza ba,” in ji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments