Hamas: Harin da aka kai a makarantar Khan Yunis da ke Gaza laifi ne na yaki

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a daren jiya a wata makaranta da ke kusa da

Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a daren jiya a wata makaranta da ke kusa da rukunin likitocin Al-Nasser da ke birnin Khan Yunis na Gaza.

A cikin bayanin da ta fitar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah-wadai da harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan hare-haren da ta kaddamar a kan  makarantar Ahmed Abdul Aziz, a wani sansanin ‘yan gudun hijirar Falasdinu da ke kusa da rukunin likitocin Nasser da ke birnin Khan Yunus a kudancin zirin Gaza, wanda ya yi sanadin shahadar  mutane sama da 20 da kuma jikkatar wasu da dama.

Galibin wadanda suka yi shahada da kuma wadanda suka jikkata a wannan harin yara ne da mata da kuma tsofaffi da kananan yara.

Kungiyar Hamas ta dauki wannan laifi a matsayin ci gaba da mummunar manufar kisan gillar da ake yi wa al’ummar Gaza, da kuma shirin kawar da makarantu da cibiyoyin tsugunar da ‘yan gudun hijira, inda ta kuma bayyana cewa: Gwamnatin Sahayoniya tana ci gaba da aikata munanan laifuka da na dabbanci ba tare da nuna damuwa daga al’ummomin duniya kan wannan ta’asa ba.

Hamas ta kuma dauki Amurka a matsayin babbar mai daukar nauyin wannan kisan kiyashi kuma mai hannu kai tsaye wajen aikata wadannan laifuka, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki mataki kan wannan zubar da jini da ake yi a Gaza a kan  idon duniya, tare da matsa lamba  a kan gwamnatin mamaya domin karshen wannan kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments