Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa gazawar Isra’ila wajen cimma burinta a Gaza ne ya tilasta mata amincewa a tsagaita wuta.
Gazawar Isra’ila wajen cimma burinta ne ya tilasta mata sassauta ra’ayinta a teburin sulhu, a cewar Mohammad Nazzal, wani babban jami’i a fannin siyasa na kungiyar Hamas.
“Burin Isra’ila shi ne ta kubutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su’’.
Babu daya daga cikin muradunta da ya biya,” in ji Nazzal a kebantacciyar tattaunawa da Anadolu Agency.
“Sun kasa yin amfani da karfin soji don kubutar da mutanensu da aka yi garkuwa da su don haka sai suka sassauta matsayinsu a lokacin tattaunawa.
A halin da ake ciki, babu yadda za a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su idan ba ta hanyar sulhu ba,” a cewarsa.