Hamas: Da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar zaman lafiya

Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da kin amincewar firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na kin amincewa da sabuwar shawarar da masu

Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da kin amincewar firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na kin amincewa da sabuwar shawarar da masu shiga tsakani suka yi na tsagaita bude wuta a Gaza.

Mamban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Bassem Naim, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar sulhun Gaza don kare kansa da kuma majalisar ministocinsa na masu tsattsauran ra’ayi, da kuma zafafa yakin da ake yi kan al’ummar Gaza.

Ya bayar da misali da rahotannin da kafafen yada labarai na baya-bayan nan da ke nuni da cewa gwamnatin kasar ta yi watsi da yarjejeniyar wani bangare da Hamas, yana mai cewa Tel Aviv na son cimma cikakkiyar yarjejeniya da goyon bayan Amurka.

Naim ya jaddada cewa, Hamas ba ta samu wani martani a hukumance kan tayin sulhu na baya-bayan nan ba, ko kuma wata sabuwar shawara kan wata cikakkiyar yarjejeniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted