Search
Close this search box.

Hamas : Babu Wani Ci Gaba A Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza Da Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bakin wani jami’inta ta bayyana cewa babu wani ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila. Osama

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bakin wani jami’inta ta bayyana cewa babu wani ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da Isra’ila.

Osama Hamdan ya ce har yanzu a shirye Hamas take a cimma matsaya  mai kyau” kan shawarar tsagaita bude wuta ta kawo karshen yakin kamar yadda ya bayyana a wani taron manema labarai a Beirut.

Hamdan ya kuma ce yunwa na ci gaba da yin barazana ga rayuwar Falasdinawa a zirin Gaza, musamman a birnin Gaza da kuma yankunan arewacin kasar, yana mai zargin Isra’ila da kin ba da izinin samar da abinci, ruwa, magunguna, da man fetur.

“Kungiyoyin kasa da kasa da dama sun tabbatar da cewa al’ummar zirin Gaza, wadanda adadinsu ya kai miliyan 2.3, na bukatar a kai a kalla manyan motocin agaji 500 a kowace rana,” in ji Hamdan.

Yanzu haka dai daukacin al’ummar Gaza na fama da karancin abinci.

Yara 346,000 ‘yan kasa da shekaru biyar na fama da tamowa.

Yara 50,400 ‘yan kasa da shekaru biyar suna fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki.

Mata masu ciki da masu shayarwa 160,000 na bukatar karin abinci don gujewa rashin abinci mai gina jiki, inji jami’in na Hamas.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments