Haifaffiyar kasar Somalia Sagal Abdi-Wali ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabuwar yar Majalisar Birtaniya da ke wakiltar Holborn a St Pancras.
Abdi-Wali mai shekaru 42 ta samu nasarar shiga majalisar ne don maye gurbin tsohon Firaminista Keir Starmer a majalisar ƴar Majalisar tsakiyar birnin London.
A Abdi wali ta shiga birtaniya ne a matsayin ƴar gudun hijira tana ƙaramar yarinya inda ta shafe ratuwarta a Camden na birnin London, tare da aiki da mabanbantan ƙungiyoyin agaji baya ga koyarwa a mabanbantan makarantu gabanin zama shugabar yanki.
Takararta na koƙarin neman wannan kujera ta ƴar Majalisa ya janyo hankalin ɗimbim ƴan Somalia mazauna Birtanita da kuma sauran ƴan kasashen Afrika da suka nuna mata goyon baya wajen kaiwa ga nasara.
A jawabinta bayan nasara, Abdi-Wali ta bayyana aniyarta ta yaƙi da matsalar rashin matsugunan da jama’a ke fama da shi baya ga bayar da cikakkiyar dama ga matasa.