Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Fara Janye Dakarunta Daga Kasar Yemen

Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara janye dakarunta daga Yemen biyo bayan wa’adin da Saudiyya ta bata na sa’o’i 24 don sojinta su fice daga Kasar,

Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara janye dakarunta daga Yemen biyo bayan wa’adin da Saudiyya ta bata na sa’o’i 24 don sojinta su fice daga Kasar, a wani sabon rikici tsakanin manyan kasashen Larabawan dake samar da man fetur.

Harin wanda Riyadh ta ce ta yi shi ne kan jirgin ruwan dake dauke da makamai wanda ke da alaka da Daular Larabawa, na nuni irin yadda alaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu.

Dubai ta ce tun shekarar 2019 ta kawo karshen zaman dakarunta dake yakar matsalar ta’addanci a Yemen, kuma kadan daga ciki ne suka rage wadannan a cewarta su na sanya ido ne kan yanayin tsaron kasar, hadin gwiwa da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa.

Tsawon shekaru kenan, Saudiyya da Daular Larabawa ke taka rawa a Yemen, inda kowannensu ke da ƴan awaren da yake goyawa baya a cikin kasar. Haka zalika, kowace kasa a cikinsu na kokarin rubanya tasirinta a Yemen , saboda dalilai na kashin kansu wanda zai amfane su ko kuma Yemen ɗin ko ma akasin haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted