ministan harkokin wajen hadaddiyar daular larabawa ya jaddada cewa ko da wasa kasarsa ba zata taba bari ayi amfani da sararin samaniyarta ko ruwanta wajen daukar matakin soji kan kasar iran ba.
acikin wani bayani da ta fitar a jiya litinin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran tace hadadiyar daular larabwa ta jaddada matsayinta na kin amincewa ayi amfani da sararin samaniyarta ko ruwanta wajen daukar matakin soji kan kasar iran, kuma ba za ta bada wani taimako na kayan aiki ba don kaddamar da harin
wadanan bayanan suna zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka take tattara kayayyakin soji a kusa da iran da suka hada da jirgin ruwan mai goya makamai na Uss Abrahman Lincoln a ruwan yammacin Asiya, inda shugaban kasar Amurka Donald trump ya fadi cewa za su yi amfani da matakin soji kan iran idan tayi amfani da karfi kan masu tada tarzoma da kona masallatai a kasar
kasashen Amurka da hukumar leken asari ta Mossad ta Isra’Ila a fili sun nuna goyon bayansu kai tsaye ga masu tada tarzoma a kasar iran, inda tsohon ministan wajen Amurka Mike Pompeo ya aike da sako a shafinsa na tweter cewa muna ma iraniyawa da suka fito kan tituna barka da sabuwar shekara, kuma dukkan jami’an Mossad suna tare da su.