Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli

Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan  Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a

Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan  Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi.

Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai.

A cikin wannan yanayi, wani bincike na Isra’ila ya nuni da karuwar masu kasha kansu a tsakanin sojojin Isra’ila tun daga lokacin fara yakin zirin Gaza. Bincike na hadin gwiwa da jami’ar Tel Aviv da sojoji suka gudanar ya nuna cewa kashi 12% na sojoji suna fama da matsalar damuwa da kunci.

Adadin wadanda suka kashe kansu tun daga watan Oktoban 2023 ya haura sojoji 43, ya zuwa ranar da aka fitar da binciken a ranar 16 ga watan Yuli, wanda ke nuna munanan yanayin da suke sakamakon ayyukan kisan kare dangi da suke kan mata da kananan yara da sauran fararen hula a Gaza.

Wani Shafin yanar gizo na Isra’ila ya bayyana cewa, asarar sojojin da Isra’ila ke yi bai takaita ga wadanda aka kashe a wurin yaki ba, hakan ya hada  har ma da sojojin da suke kashe kansu saboda damuwa, da kuma masu mutuwa sakamakon raunuka da suka samu.

Bayanai sun nuna cewa sojoji 15,000 ake kula da su sakamakon matsalolin ad suka samu a wajen yaki, kashi 35% daga cikinsu suna fama da matsaloli na kunci da damuwa ko kuma tabuwa ta hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted