Haramtacciyar Kasar Isra’ila da gwamnatin Saudiyya sun yi nisa a tattaunawar da suke yi domin kulla alaka a tsakaninsu a hukumance, kamar yadda jaridar Haaretz ta Isra’ila ta tabbatar a wani rahoto da ta rubuta.
Majiyoyin da ke cikin tattaunawar sun bayyana cewa Saudiyya ta janye sharadin da ta gindaya a baya kan cewa sai a samar da kasar Falastinu mai cin gashin kanta kafin ta amince da kulla alak a hukuamnce tare da Isra’ila.
A cewar jaridar, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ba shi da wata maslaha ta kashin kansa wajen amincewa da kasar Falasdinu a hukumance, sai don kawai yana bukatar ci gaba da samun samun goyon bayan siyasa da na addini a cikin gida da kuma wajen kasashen musulmi.
Tattaunawar bangarorin biyu ta kara bunkasa a ‘yan makonnin nan, bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma da kasar Lebanon. Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ne ke jagorantar tattaunawar ta hannun ministan kula da tsare-tsare Ron Dermer, inda aka ce yawancin jami’an gwamnatin Isra’ila da majalisar ministoci, da jami’an tsaro ba su da masaniya kan yadda tattaunawar take gudana tsakanin Saudiyya da Isra’ila.
Amurka ce ke shiga tsakani a tattaunawar, inda gwamnatin Joe Biden da zababben shugaban kasar Donald Trump ke taka muhimmiyar rawa. Ana sa ran Saudiyya za ta sami tabbacin Amurka, da hakan ya hada da yarjejeniyar tsaro da samun damar yin amfani da na’urorin sarrafa makaman Amurka na zamani, a wani bangare na yarjejeniyar.