Gwamnatin ‘Yan Mamaya Ta Karyata Kanta Dangane Da Labarin Kashe Al-Deif A Al-Mawasi

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta janye da’awar cewa ta kashe Muhammad al-Deif a hare-haren kisan kiyashin da ta kai kan garin Al-Mawasi na Falasdinu A

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta janye da’awar cewa ta kashe Muhammad al-Deif a hare-haren kisan kiyashin da ta kai kan garin Al-Mawasi na Falasdinu

A jiya Lahadi ce sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka janye da’awar karyarsu ta cewa sun aiwatar da kisan gilla kan babban kwamandan rundunan shahidan Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Muhammad al-Deif, a yayin wani kazamin kisan kiyashi da suka aikata jiya a garin Al-Mawasi da ke yankin yammacin birnin Khan Yunus a kudancin Zirin Gaza.

Gidan rediyon sojojin yahudawan sahayoniyya ya nakalto daga majiyar tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Babu wata madogara mai tushe ta hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke tabbatar da nasarar yunkurin kisan gillar da aka shirya kan Muhammad Al-Deif babban kwamandan rundunan shahidan Izzuddeen al-Qassam.

Gidan rediyon sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi ikirarin cewa: Babban kwamandan rundunar Izzuddeen al-Qassam Muhammad Al-Deif tun farkon fara yaki kan Gaza ya kasance a garin Khum Yunus da ke shiyar kudancin Zirin Gaza, kuma a mafi yawan lokuta yana cikin ramukan ƙarƙashin ƙasa, sannan a yayin wani hari ta sama da aka kai kan tantunan ‘yan gudun hijirar Falasdinawa a yankin Al-Mawasi da ke yammacin birnin Khan Yunis a ranar Asabar din da ta gabata, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 90 ciki har da Al-Deif da mataimakinsa tare da jikkata wasu 300 na daban da suka hada da kananan yara da mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments