Gwamnatin Yamen Ta Ce Tana Iya Kai Hare Hare A Wuraren Da Makiya Basu Zata Ba

Kakakinn sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree ya bayyana cewa mai yuwa sojojin kasar su kai hare hare a kan wuraren da makiya basu

Kakakinn sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree ya bayyana cewa mai yuwa sojojin kasar su kai hare hare a kan wuraren da makiya basu zata ba.

Tashar talabijin ta Almasira ta kungiyar Ansarallah ta kasar, ta nakalto Janar Saree yana fadar haka a jiya litinin. Ya kuma kara da cewa da alamun HKI bata son dawo da zaman lafiya a Gaza nan kusa, saboda tana kara takurawa falasdinawa a yankin kusan a ko wace rana.

Ya ce, al-amarin gaza,  jan layi ne a wajemmu, wurare masu tsarki a kasar Falasdinu da aka mamaye jajayen layi ne a wajemmu, don haka ba zamu taba kauda hankali daga barinsu ba.

Daga karshe Burgedia Yahyah Saree ya ce, idan wannan halin ya ci gaba mai yuwa sojojin kasar Yemen su kai hare hare kan wuraren da makiya basu zata ba, hatta mutanen kasar Yemen basu zata sojojin kasar suna da karfin yin haka ba.

Sojojin kasar Yemen dai sun shiga yaki da HKI da kuma kawayenta ne tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai sojojinn yahudawan sun kashe Falasdinawa kimani 35,000 mafi yawansu mata, sannan sun raunata wasu kimani dubu 78.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments