Kasar Sudan ta bayyana matsayinta kan harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Iran
Gwamnatin Sudan ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Iran, tana bayyana harin a matsayin cin zarafi a fili ga ‘yanci da jagorancin kasar ta Iran.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fitar ta bayyana cewa: Ma’aikatar harkokin wajen Sudan tana adawa da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana matsayin keta hurumin kasar Iran, da dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya na kasa da kasa da kwanciyar hankalin duniya.
Har ila yau ma’aikatar ta yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-hare kan kasashen Lebanon da Siriya da kuma ci gaba da cin zarafi da haramtacciyar kasare Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu.