Gwamnatin Sudan Ta Sanar Da Komawa Birnin Khartoum A Hukumance

Gwamnatin Sudan ta dawo Khartoum babban birnin kasar a hukumance a karon farko tun bayan barkewar rikicin shekarar 2023, Firayim Ministan Sudan, Kamel Idris ne

Gwamnatin Sudan ta dawo Khartoum babban birnin kasar a hukumance a karon farko tun bayan barkewar rikicin shekarar 2023, Firayim Ministan Sudan, Kamel Idris ne  ya sanar da hakan.

Da yake jawabi ga taron ‘yan kasar bayan sun isa daga Port Sudan, inda gwamnati ke aiki na wucin gadi, Idris ya bayyana matakin a matsayin “wani muhimmin lokaci” ga kasar.

Ya ce, “A yau za mu dawo, kuma tare da da ku za mu dawo da gwamnatin kasa  zuwa babban birnin kasar. Mun yi alkawarin inganta ayyuka da inganta rayuwar mutanenmu.”

Idris ya yi alÆ™awarin farfado da fannin lafiya da ilimi, sake gina asibitoci, da kuma gyara makarantu da jami’o’i, tare da mai da hankali kan Jami’ar Khartoum. Ya kuma yi alÆ™awarin inganta tsaro da yanayin rayuwa ga ‘yan kasa.

Wannan matakin ya biyo bayan sake kwace Khartoum da sojojin Sudan suka yi a watan Mayu, bayan kazamin fada a yankin Al-Salaha da ke kudancin birnin.

A watan Yuli, Shugaban Majalisar Mulkin Soja ta Wucin Gadi, Abdel Fattah al-Burhan, ya bayar da wata doka da ta kafa kwamitin kasa don shirya komawa  Khartoum da cibiyoyin tarayya da mazauna birnin  cikin gaggawa.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted