Mutane 22 ne suka mutu sakamakon hare-haren jiragen saman yakin Pakistan kan larduna biyu na kasar Afghanistan
Gwamnatin Pakistan ta sanar da kashe mutane 22 da ta bayyana a matsayin ‘yan ta’adda” a hare-haren jiragen sama da ta kai kan yankunan kasar Afghanistan, baya ga lalata makamai da harsasai masu yawa.
Wata majiyar gwamnatin Afghanistan ta shaida wa gidan talabijin na Al Jazeera cewa: Mutane tara sun mutu yayin da wasu bakwai suka jikkata a hare-haren jiragen saman Pakistan a lardunan Kunar da Helmand.
Kamar yadda shugaban sashin watsa labarai da al’adu na Helmand, Maulvi Sher Mohammad Wahdat, ya shaida wa Reuters a ranar Alhamis, jiragen sama na Pakistan sun kai hare-hare ne kan gidaje biyu a gundumar Garmsir da ke lardin.
A bisa kididdigar farko, an kashe mutane hudu yayin da wasu shida suka jikkata zuwa yanzu. Yawancin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata mata ne da yara,” in ji Wahdat, a cewar Reuters.