Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A karkashin Sashe na II, bangare na 4 na dokar, dukkan mutane da kungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card).
Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin wadanda suka gaza yin rajista, ko su ki karbar bukata idan bayanan da ake da su sun nuna hakan ya dace. Dole ne a sanar da mai nema duk wata cikin kwanaki biyar na aiki.