Gwamnatin Najeriya Ta Bada Cikekken Tsarin Yadda Za’a Yi Jana’izar Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura tawagar manya-manyan Jami’an gwamnati 25 zuwa jihar Katsina don halattar Jana’izan da za’a yiwa tsohon shugaba marigayi Muhammadu Buhari jana’iza.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura tawagar manya-manyan Jami’an gwamnati 25 zuwa jihar Katsina don halattar Jana’izan da za’a yiwa tsohon shugaba marigayi Muhammadu Buhari jana’iza.

Jaridar Premium times ta sami sanarwa wacce ministan yada labarai Mohammed Idris  ya sanyawa hannu yana cewa tawagra zata ci gaba da zama a Daura na jihar katsina har zuwa kwanaki uku da za’a ya masa addu’a ta karshe  da za’a yi masa.

Buhari ta zama shugaban kasar Najeriya har sau biyu, daga watan jenerun shekara 2015-2023, sannan kafin haka ya rike kasar daga 1984-1985.

A makon da ya gabata ne ya je birnin Londan na kasar Burtania amma sai rai yi halinsa a shekaran jiya. A yau ne za’a yi masa da jana’iza da bisalin karfe 2 na rana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted