Gwamnatin Kasar China Ta Ji Dadin Tsagaita Wuta Tsakanin Hamas Da HKI

Ma’aikatar harkokokin wajen kasar China ta bayyana jin dadinta da tsagaita wuta a Gaza, kuma tace tana goyon bayan aiwatar da ita kamar yadda aka

Ma’aikatar harkokokin wajen kasar China ta bayyana jin dadinta da tsagaita wuta a Gaza, kuma tace tana goyon bayan aiwatar da ita kamar yadda aka tsara. Sannan tace kasar Chain zata taimaka da ayyukan jinkai ga Falasdinawa bayan an aiwatar da yarjeniyar tsagaita wutar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Geo Chia Kan, yace kasar China ta yi farinciki da kawo karshen zubar da jinin mutanen Gaza, kuma zata taimaka wajen gabatar da kayan jinkai da kuma abubuwan da za su zo na bayan tsagaita wuta wadanda suka hada da sake gina yankin zirin gaza.

Kan, ya yi kira ga bangarorin biyu sun yi amfani da wannan damar don samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu. Ana saran a ranar farko na aiwatar da yarjeniyar kayakin agaji masu yawa zasu shigo zirin gaza daga kudu har zuwa arewacin yankin don fara tallawa wadanda suke mummunan hali. Sannan za’a sake gina wurare masu muhimmanci na da farko wato Asbitoci da makarantu da gidajen bredi da tentuna masu inginci don karesu Falasdinawa daga sanyi da ke kashe yara kanana.

Falasdinawa 46,700 ne sojojin HKI suka kashe tun ranar 7 ga watan Octoban 2023. Sannan wasu fiye da 100,000 kuma suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments