Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun lalata asibitin Mohammed Yousef al-Najjar da ke Rafah a kudancin zirin Gaza, ta hanyar amfani da wasu motocin yaki marasa matuka.
Dr. Marwan al-Hams, Darakta-janar na asibitocin filayen a yankin da aka yiwa kawanya ya bayyana cewa, barnar da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi asibitin gwamnati hakan ya zo daidai da tsarin da Isra’ila ke bi ne wajen kai wa kayayyakin kiwon lafiya hari a Gaza.
Ya bayyana cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun tura wasu bama-bamai masu fashewa don lalata wurin jinya.
Asibitin ya ba da sabis na kiwon lafiya da lafiya ga mutane 300,000,” in ji al-Hams.
Ya kara da cewa, “Asibitin ya yi hidima ga sama da mutane miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu da sauran jama’a mazauna zirin Gaza, kafin mamayar da yahudawa suka yi wa lardin Rafah,” in ji shi.
Jami’in kiwon lafiyar ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai da dace domin kare da kuma da kuma farfado da fannin kiwon lafiya na zirin Gaza.
A halin da ake ciki dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan ma’aikatan lafiya da na agajin gaggawa a duk fadin yankin zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ba da rahoton cewa, “an lalata asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da dama lamarin da yasa suka tsaya cak ba tare da iya bayar da hidima ga marasa lafiya ba.