Gwamnatin Iraqi Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta Ga Rundunar Sa-Kai Ta Hashdus-Sha’abi

Fira ministan kasar Iraki Muhammad Shiya’al-Sudani wanda ya gabatar da jawabi a wurin bikin zagayowar shahadar jagororin gwgawarmayar kasar, ya bayyana goyon bayan gwamnatin kasar

Fira ministan kasar Iraki Muhammad Shiya’al-Sudani wanda ya gabatar da jawabi a wurin bikin zagayowar shahadar jagororin gwgawarmayar kasar, ya bayyana goyon bayan gwamnatin kasar akan rundunar sa-kai ta Hashdus-shabai.

 An yi bikin zagayowar lokacin shahadar jagororin gwgawarmayar ne da su ka hada janar Sulaimani da Injiniya Abu Mahdi  a birnin Bagadaza da can ne inda su ka yi shahadar.

Manyan ‘yan siyasar kasar ta Iraki ne su ka halarci taron tare da gabatar da jawabai akan rawar da shahidan su ka taka wajen murkushe ‘yan ta’adda a cikin Iraki.

Fira minista Al-Sudani ya ce, a kodayaushe a lokacin rayuwarsa, Injiniya Abu Mahdi ya kasance mai bayar da goyon baya ga gwamnati, kuma rundunar  “Hashdus-sha’abi’ wani bangare ne na gwamnati, tana kuma tafiyar da ayyukanta ne a karkashinta, kuma a yanzu an wayi gari ta zama mai karfi a siyasance da take kare kasar ta Iraki.

Sudan ya kuma kara da cewa; “Gwamnatina tana son karfafa rundunar sa-kai din ta Hashdu-Sha’ani da kare tabbatar da ita a matsayin wata cibiya ta tsaro daidai da sauran hukumomin tsari, domin ta taka rawa wajen samar da tsaro da hakan ya bai wa gwamnati damar aiwatar da ayyuka cigaban kasa da su ka hada da fagen tattalin arziki a ko’ina a cikin kasa.”

Shi kuwa shugaban rundunar sa-kai din ta Hashdu-Sha’abi, Falih Fayyadh ya bayyana cewa; Rundunar tasu dai ta sami halarcinta ne  daga kasantuwarta wani bangare na al’ummar kasar, domin tana kare al’ummar Iraki ne a cikin iyakokin wannan kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments