Gwamnatin HKI Ta Amince Da Yarjeniyar Sulhu Da  Tsagaita Wuta Da Kungiyar Hamas A Gaza

Majalisar dokokin HKI ta amince da yarjeniyar dakatar da budewa juna wuta a Gaza tsakanin haramtacciyar kasar da kuma kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. Tashar talabijin

Majalisar dokokin HKI ta amince da yarjeniyar dakatar da budewa juna wuta a Gaza tsakanin haramtacciyar kasar da kuma kungiyar gwagwarmaya ta Hamas.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Benyamin Natanyahu yana fadar haka, ya kuma kara da cewa tsagaita budewa juna wutan da kuma musayar fursinoni zai fara aiki ne a gobe Lahadi.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne jiragen yakin HKI suka fara kaiwa Falasdinawa a gaza hare-hare, wanda ya kai ga mutuwar falasdinawa 46,788 bayan fafatawa na kimanin  kwanaki 460 mafi yawansu mata da yara ne.

Natanyahu ya kara da cewa daga gobe Lahadi ne ake saran karban fursinonin yaki daga kungiyar ta Hamas, a yayinda su kuma zasu karbi wasu Falasdinawa.

Gwamnatin Benyamin Natanyahu dai ta sha alwashin ba zata kawo karshen yakin ba sai ta kaiga dukkan manufofin yakin gaba daya.

Daga cikin har da wargaza kungiyar Hamas daga doron kasa, da kuma kubutar da yahudawan kimani 100 guda da suke tsare a hannun mayakan Hamas tun lokacin fara yakin.

Musaya ta farko dai zai kasance ne tsakanin Yahudawa 33 da kuma Falasdinawa 1,977, kuma za’a kammala musayar da kuma ficewar sojojin HKI daga gaza ne cikin kwanaki 42.

Sannan tsagaita wutan da farko na makonni 6 ne, sannan ana iya tsawaitata zuwa tsagaita wuta na din din din.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments