Gwamnatin Gaza Ta Bukaci Tawagar WHO Da Ta Ziyarci Asibitin Kamal Adwan

Gwamnatin Gaza ta bukaci Hukumar Lafiya ta Duniya da ta gaggauta tura tawaga don kare Asibitin Kamal Adwan da ma’aikatansa da marasa lafiya da Falasdinawa

Gwamnatin Gaza ta bukaci Hukumar Lafiya ta Duniya da ta gaggauta tura tawaga don kare Asibitin Kamal Adwan da ma’aikatansa da marasa lafiya da Falasdinawa da suka rasa muhallansu daga hare-haren Isra’ila. 

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce harin barazana ne ga asibitoci kuma laifi ne na bil adama da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce “Wadannan hare-haren na ci gaba da gudana kuma ba su tsaya ba kusan kwanaki 80 tun lokacin da aka fara kai hare-hare ta kasa kan yankin arewacin zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, da bacewar wasu da dama, ko jikkata ko kuma tsarewa.”

Ofishin ya kara da cewa harin da aka kai wa asibitin Kamal Adwan wani bangare ne na shirin Isra’ila na ruguza tsarin kiwon lafiya a yankin.

Bayanai sun ce sojojin Isra’ila sun kashe mutane 32 a rana guda, a harin na asibitin Kamal Adwan.

Gwamnatin Gaza ta ce ta dora alhakin harin na Isra’ila da hadin guiwar Amurka da sauran kasashe da ke da hannu a “kisan kare dangi” kamar Jamus, Burtaniya da Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments