Gwamnatin Amurka Tana Boye Hasarar Da Take Yi A Yaki Da Iran

Wani sanatan Amurka ya bayyana cewa: Tabbas Amurka ta yi hasarar biliyoyin daloli a sansanoninta da suke Qatar da Bahrain Sanata Chris Murphy na Amurka

Wani sanatan Amurka ya bayyana cewa: Tabbas Amurka ta yi hasarar biliyoyin daloli a sansanoninta da suke Qatar da Bahrain

Sanata Chris Murphy na Amurka ya bayyana hasarar da sansanonin sojin Amurka suka yi a Qatar da Bahrain, yana mai sukar abin da ya bayyana a matsayin boye gaskiya ga jama’ar Amurka game da girman hasarar da aka yi da kuma kudin yakin.

Kamfanin dillancin labaran Mehr, ya watsa rahoton cewa: Sanata Chris Murphy na Amurka ya bayyana bayanan da ya fitar game da barnar da aka yi wa sansanonin sojin Amurka a yankin Tekun Farisa bayan an hana su shiga wadannan sansanonin saboda munanan hare-hare.

Murphy ya tabbatar da cewa: Sansanonin sojin Amurka a Qatar, da kuma sansanin sojin Amurka a Bahrain, sun yi hasarar da aka kiyasta ta kai biliyoyin daloli.

Sanatan na Amurka ya nuna cewa: Amurka ta gaza a wannan yakin da daura kan Iran, ganin abin da ke faruwa abin kunya ne ga jama’ar Amurka.

Ya kara da cewa: Akwai wani shiri da aka shirya da nufin boye gaskiyar lamarin ga Amurkawa da kuma hana su sanin ainihin girman hasarar da kuma yawan kudaden da ake kashewa a yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted