A Guinea an ayyana zaman makoki na kwanaki uku biyo bayan turmutsitsin da ya yi ajalin gomman mutane a filin wasan kwalon kafa na yankin N’Zérékoré.
Kazamin turmutsitsin ya faru ne a ranar Lahadi a filin wasa na ranar 3 ga watan Afrilu yayin wasan karshe na gasar kwallon kafa da aka shirya domin nuna goyon baya ga shugaban rikon kwarya Mamadi Doumbouya.
Gwamnati ta ba da sanarwar mutuwar mutane 56 na wucin gadi.
Wasu bayanai na daban sun ce mutane fiye da 100 ne suka mutu yayin da gommai suka jikkata bayan wani rikicin da ya barke ranar Lahadi yayin gasar kwallon kafa a kudu maso gabashin kasar.
Rikicin ya barke ne bayan magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Labe sun ki amincewa da kwallon da kungiyar Nzerekore ta zura musu, lamarin da ya kai ga taho-mu-gama a Nzerekore, birni na biyu mafi girma a kasar, wanda ke da nisan kilomita kusan 570 daga Conakry, babban birnin kasar, a cewar jaridar Mediaguinee.
Hukumomin kasar dai sun ce suna gudanar da binkice kan lamarin da kuma irin barna da hasarar rayukan da aka samu.