Jirgin Ruwan Da Ya Saba Doka Ya Kama Da Wuta A Tekun Hormuz

Sojojin Iran sun sanar da cewa: Gobara ta tashi a wani jirgin ruwan dakon mai da ya karya dokoki a kudancin mashigar ruwan Hormuz Ofishin

Sojojin Iran sun sanar da cewa: Gobara ta tashi a wani jirgin ruwan dakon mai da ya karya dokoki a kudancin mashigar ruwan Hormuz

Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Iran ya sanar da cewa: Wani jirgin ruwan dakon mai ya kama da wuta a yankin tekun mashigar Hormuz a wata hanya da aka hana bi a kudancin mashigar ta Hormuz.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr na kasar Iran, Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Ruwa ta Iran ya ce: “A safiyar yau, ƙungiyoyin sa ido na Rundunar Sojin Ruwa ta Iran, waɗanda ke ci gaba da sa ido da kuma iko da gabashin mashigar Hormuz, sun gano wani jirgin ruwan mai da ke ƙonewa a yankin da aka hana bi ta cikinsa.”

“Duk da gargaɗin da aka yi a baya, wannan jirgin ruwan ya karya tsarin dokar bin hanya da aka kayyade, don haka ya yi ƙoƙarin ratsa yankin da aka hana bi a kudancin mashigar Hormuz.”

Rundunar Sojin Ruwa ta Iran ta jaddada cewa: Mummunan sakamakon zirga-zirgar jiragen ruwa ba tare da tsari ba yana hannun waɗanda suka karya doka, kuma wannan rashin haɗin kai ya haifar da rashin zaman lafiya a ko’ina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted