Sabon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya nada manzon musamman a kungiyar kawancen kasashen Sahel.
Larry Gbevlo-Lartey, tsohon babban hafsa a rundunar sojojin Ghana, wanda kuma ya taba jagorantar yaki da ta’addanci a cikin kungiyar Tarayyar Afirka, shi ne aka dora wa alhakin karfafa dangantakar Ghana da kasashen mambobin AES.
Nada manzon na musamman tsakanin Ghana da kasashen na Sahel da sojoji ke mulki, na da zummar samar da manufofin bai daya kan yaki da ta’addanci, samar da abinci da zirga-zirgar kayayyaki da jama’a cikin ‘yanci shi ne babban aikin da aka damka wa Larry.
manzon musamman na shugaba John Dramani Mahama zuwa ga AES. “A cikin ‘yan shekarun nan, wannan dangantakar ba ta da ƙarfi sosai.
Matakin na Ghana bai da alaka da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, (ECOWAS-CEDEAO) wacce ake sa ran za ta tabbatar da ficewar kasahen na Burkina Faso, Mali da Nijar a hukumance a wannan Laraba, 29 ga watan Janairu.
Larry ya tabbatar da cewa batun ko mayar da kasashen a cikin kungiyar ECOWAS bai cikin ajandarsa hasali ma matakai na ‘yanci da Burkina Faso, Mali da Nijar suka dauka.
Wannan ba batu ne ba da Ghana ta kamata ta sa baki a ciki, kuma ba batun da muka fifita ba ne.
Aikin farko na manzo na musamman ga kasashen na sahel: ba da damar shiga tashar ruwa ta Tema ta Ghana ga kasahen da basu da tashar ruwa.