Ghana : John Dramani Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Sabon Shugaba

Zababen shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi rantsuwar kama aiki a bikin da aka gudanar a Accra babban birnin kasar. Shugabannin kasashe 21,

Zababen shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi rantsuwar kama aiki a bikin da aka gudanar a Accra babban birnin kasar.

Shugabannin kasashe 21, ne suka halarci bikin rantsarwar.

A watan Disamban 2024 ne ya lashe zaben shugabancin kasar da kashi 56.55 na kuri’un da aka kada, inda ya kayar da Mataimakin Shugaban Kasa Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP mai mulki.

Mista Mahama ya taba mulkar kasar daga shekarar 2012 zuwa 2017.

Zababen shugaban kasar ya sha alwashin mayar da hankali kan farfado da kasar daga matsalar tattalin arziki.

Dangane kuma da yaki da cin hanci da rashawa, John Dramani Mahama ya ce zai bai wa hukumomi masu yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu.

Ya kuma ya sha alwashin yi wa kundin tsarin mulkin garambawul wajen rage kudaden da ake bai wa shugabanni da kuma daidaito a albashin dukkanin ma’aikatan gwamnati.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments