Gaza: ‘Yan Gwagwarmaya Sun Tarwatsa Motocin HKI Da Dama

Dakarun rundunar gwgawaraya ta “Kudus” reshen kungiyar Jihadul-Islami sun  sanar da kai hari akan motoci da dama na sojojin mamaya. Rundunar ta “Kudus”  ta fitar

Dakarun rundunar gwgawaraya ta “Kudus” reshen kungiyar Jihadul-Islami sun  sanar da kai hari akan motoci da dama na sojojin mamaya.

Rundunar ta “Kudus”  ta fitar da wani faifen bidiyo da ta nuna yadda mayakanta suke dasa bom mai tarwatsa tankokin yaki da kuma wasu motocin daukar soja a sansanin  Jabaliya dake arewacin Gaza.

Bugu da kari bidiyon ya nuna lokacin da motocin na sojojin mamaya su ka taka wata  nakiya wacce ta tarwatse da su.

Arewacin Gaza yana daga cikin inda HKI take tsananta kai hare-hare da zummar korar Falasdinawa daga cikinsa saboda ta kafa shingen tsaro tsakaninta da mutanen Gaza. Bugu da kari sojojin mamayar sun rusa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da suke a wannan yankin,na karshensu shi ne asibitin “Kamal Adwan”.

A gefe daya kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da wata sanarwa a yau Juma’a zuwa ga iyalan frusunonin da suke rike da su, tare da dorawa fira minista Benjemine Netanyahu alhakin kashe fursunonin da ake rike da su a zirin Gaza.

Sakon wanda yake Magana da iyalan frusunonin ya kunshi cewa: Jagororinku ne suke kashe ‘yan’yanku cikin sani.”

Bayan wannan rubutaccen sakon, an nuna hare-hare masu muni da jiragen HKI suke kai wa  yankin Gaza,sai kuma sautin fursunonin da suke kara da karfi,alamar harin da aka kai wa Gaza ya shafi inda suke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments