Sojojin Isra’ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta na kwanaki uku a yakin zirin Gaza domin ba da damar yin allurar rigakafin cutar shan inna ga yara kimanin 640,000, in ji wani babban jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya.
Rik Peeperkorn, wakilin WHO a yankunan Falasdinawa, ya ce abin da ake kira “tsagaita wutar na jin kai” zai fara ranar Lahadi a tsakiyar Gaza kuma zai kai sa’o’i takwas ko tara a kowace rana na kwanaki ukun.
Matakin yana da nufin yiwa yara 640,000 ‘yan kasa da shekaru 10 rigakafin, kamar yadda Mista Peeperkorn ya fadawa manema labarai ta kafar bidiyo.
“Muna bukatar wannan dakatarwar jin kai,” in ji shi, don haka muna sa ran cewa dukkan bangarorin za su tsaya kan hakan.”
Hukumar ta WHO ta jaddada cewa ya kamata a yi wa akalla kashi 90% na yara a Gaza allurar rigakafin cutar shan inna.
Hamas ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na tsagaita wuta a yakin da Isra’ila take yi a Gaza don aiwatar da allurar rigakafin ta polio.
Jami’in Hamas Basem Naim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kungiyar a shirye take ta ba da hadin kai ga kungiyoyin kasa-da-kasa.