Bayanai daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 11 a wani hari ta sama da suka kai kan wata makaranta da ke zama wurin mafaka a zirin.
An kai harin ne a makarantar Sabad da ke unguwar Zeitoun a birnin Gaza a ranar Lahadin, kamar yadda wata majiyar lafiya ta sanar.
Majiyar ta kara da cewa adadin mutanen Gazan da suka mutu a harin bam din da Isra’ila ta kai a makarantar ya karu daga 6 zuwa 11, tare da bayyana cewa wadanda suka samu raunuka an kai su asibitin al-Ahli Arab da ke birnin Gaza.
Tun farkon yakin na Isra’ila a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, gwamnatin ta ci gaba da kai hare-hare kan ababen more rayuwa, ciki har da makarantun da ke dauke da mutanen da suka rasa matsugunnai, asibitoci da wuraren ibada, da suke zargi da alaka da Hamas.