Sojojin HKI sun kashe Karin wani dan jarida a gaza wanda ya kawo adadin yan jarida da sojojin yahudawan suka kashe tun fara yakin a ranar 7 ga watan Octoba zuwa 151.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ofishin yan jaridu da ke gaza na fadar haka a yau litinin. Yakuma kara da cewa sojojin yahudawan sun kashe Mahmood Qaseem dan jirida mai daukar hoto, kuma wadanda yake aiki tare da jaridar ‘Palastinian Daliy’ a wani harin da suka kai ta sama a zirin na gaza.
Wannan yana faruwa ne duk tare da cewa dokokin kasa da kasa sun hana kissan yan jarida a yaki, amma HKI ta sha aikata irin wadannan laifuffuka ba tare da an tanka mata ba.
Jami’an MDD sun sha Magana kan kissan yan jarida wanda HKI take yi a gaza, amma kuma ba wanda yake daukar mataki na hanata yin hakan, don haka ne kissan yan Jaridu a gaza ya zama ba alifi ne ba.
Kwamitin kare yan jaridu na kasa da kasa ya bayyana cewa ba’a taba kashe yan jaridu a wani rikici a tarihi kamar yadda HKI ta kashe yan jarida a tsakanin 7 ga watan Octoba na shekarar da ta gabata zuwa yanzu ba.