Radiyon Sojan HKI ya bayar da labarin dake cewa; An kashe wadannan sojojin ne a cikin yankin Jabaliya dake arewacin Gaza da sojojin na mamaya suka killace shi na tsawon lokaci tare da kai hare-hare masu tsanani.
Radiyon na sojojin HKI ya kuma ce a jiya Lahadi ma an kashe wasu sojojin biyu a Jabaliyan da daya daga cikinsu shi ne Yuval Shoham wanda yake a karkashin balatiya ta 9. Bugu da kari majiyar ta ce wani Karin sojan na rundunar Nahal ya sami rauni mai tsanani a fadan da yake cigaba a Arewacin Gaza.
Kashe sojojin na jiya ne dai ya cika adadin ‘yan mamayar da aka kashe a cikin Jabaliya zuwa 40 daga watan Oktoba zuwa yanzu.
Jaridar “Times” ta Isra’ila ta ce; Daga lokacin da aka fara kai farmaki ta kasa akan yankin Gaza,wannan runduna ta Nahal ta rasa sojojinta 394 daga cikinsu har da kwamandoji.
Kafafen watsa labarun HKI sun ce tun daga farmakin Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, an kashe musu sojoji 820. Haka nan kuma wasu 5,000 sun jikkata a tsawon lokacin yakin Gaza.
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa dai sun ce adadin da HKI take fada kadan ne idan aka kwatanta da yawan sojojin mamayar da su ka kashe.