Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a yau Juma’a, inda ta kai munanan hare-hare kan yankunan fararen hula da

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a yau Juma’a, inda ta kai munanan hare-hare kan yankunan fararen hula da sansanonin ‘yan gudun hijira.

Wadannan hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu a fadin yankin, lamarin da ke kara zurfafa damuwar da ake da ita game da mawuyacin da al’ummar yankin suke ciki.

Kamfanin Nasser Medical Complex ya bayar da rahoton a wannan  Juma’a cewa, wani harin da jiragen saman Isra’ila suka kai kan tantunan da mutane suke fakewa a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Khan Younis, ya kashe mutane hudu tare da jikkata wasu da dama.

A wani harin  na daban a kusa da Morag a kudancin birnin Gaza, an kashe mutane biyu tare da jikkata wasu sama da 70 da ke neman agaji.

A wani harin da aka kai a yankin Ard al-Fara da ke kudancin Khan Younis, an kashe fararen hula uku da suka hada da yaro daya da mace daya a lokacin da aka kai hari kan tantunan ‘yan gudun hijira.

A yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza kuwa Isra’ila ta kashe mutane hudu tare da jikkata wasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted