Gaza: Mutane Biyu Sun Yi Shahada A Birnin Gaza Da Khan-Yunus

Gaza: Mutane Biyu Sun Yi Shahada A Birnin Gaza Da Khan-Yunus
gawar shahidi

 A ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, sojojin mamayar Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hare-hare a birnin Gaza da kuma a Khan-Yunus wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 2 da jikkata wasu da dama.

Majiyar mutanen yankin da aka kai wa harin ta ce; Wani jirgin sama maras matuki na ‘yan mamaya ya kai hari a tsakiyar birnin Khan-Yunus da hana ya yi sanadiyyar shahadar Abu Ma’arus da kuma jikkatar wasu falasdinawa da dama.

Majiyar ta ce motocin daukar marasa lafiya ta isa wurin da aka kai wa harin domin daukar shahidai da kuma wadanda su ka jikkata zuwa asibirin Nasir.

A yankin Jabaliya dake arewacin Gaza ma wata mace ta jikkata sanadiyyar harin na ‘yan sahayoniya a kusa da shatale-talen “Abu Sharkh.

Majiyar Asibiti a yankin Gaza ta sanar da cewa daga fara yakin Gaza adadin wadadna su ka yi shahada sun kai 73,914, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 174,952.

Majiyar ta kuma ce; Tun da aka tsagaita wutar yaki kuwa a ranar 11 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata, sun kai 1,394,yayin da adadin wadanda su ka jikkata ya kai 4,839. Haka nan kuma an yi nasarar zakulo da shahidai 834.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted