Gaza: Mutane 26 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa, a cikin sa’o’i da su ka gabata Falasdinawa 26 sun yi shahada, yayin da wasu 68

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa, a cikin sa’o’i da su ka gabata Falasdinawa 26 sun yi shahada, yayin da wasu 68 su ka jikkata saboda hare-haren sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

An kai wadannan shahidan da kuma wadanda su ka jikkata zuwa asibitocin Gaza ne a cikin sa’o’I 24 da su ka gabata,kuma har yanzu da akwai wasu da suke kwance a karkashin baraguzan da aka rusa gidaje akan mutanen da suke cikinsu.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinu ta kuma ce, tun daga lokacin da aka sanar da dakatar da yaki, an sami shahidai 523, sai kuma wani adadi na mutanen da ya kai 1,443 da su ka jikkata.

Haka nan kuma a wannan tsakanin an iya fito da gawawwakin wasu shahidan 715 daga karkashin gine-ginen da aka rusa a lokacin yaki.

 Daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa ya kai 71,795, wadanda su ka jikkata kuma sun kai 171,551.

A gefe daya kasashen larabawa da na musulmi 8 sun fitar da sanarwa da cikin suke yin Allah wadai da yadda “Isra’ila” take ci gaba da keta wutar yaki a Gaza.

Kasashen da su ka sa hannu akan sanarwar su ne; Masar, UAE, Jordan, Indonesia, Pakistan, Turkiya, Saudiyya da Qatar.

Bayanin ya yi Ishara da yadda fiye da Falasdinawa 1000 su ka yi shahda da kuma jikkata tun bayan tsagaita wutar yaki,tare da bayyana hakan a matsayin lamari mai hatsarin gaske wanda zai kara dagula al’amurra a wannan yankin. Haka nan kuma sanarwar ta yi kira ga dukkanin masu bakin fada da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu domin komawa aiki da tasagita wuta da Isra’ilan take ketawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted