Falasdinawa da dama ne su ka yi shahada, yayin da wasu kuma su ka jikkata sanadiyyar hare-haren keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; An sami shahidai 5 da kuma jikkatar wasu da dama a wani hari da ‘yan sahayoniya su ka kai a wani wurin shan shayi dake yammacin birnin “Deir-Balah” dake tsakiyar yankin Gaza.
Haka nan kuma tashar talabijin din ta ce sojojin mamayar sun kai wani harin a garin Zuwaidah, dake tsakiyar zirin Gaza da ya jikkata mutane da dama.Wasu Karin hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi binin Rafah, da Jabaliya.
Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojojinsu sun kai wasu hare-hare har 20 a Gaza.
A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin shahidan Falasdinawa sun kai 8, yayin da wasu 10 da su ka jikkata.
Kididdigar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce daga 7/10/2023 zuwa yanzu jumillar shahidan Falasdinawa sun kai 68,159, sai kuma wasu 17,203 da su ka jikkata.
A gefe daya ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta sanar da karbar shahidai 15 da HKI ta mika gawawwakinsu a karkashin yarjejeniya, da hakan ya sa jumillar adadin shahidan da su ka karba zuwa 150.
A wani labarin na daban, HKI ta bayar da umarnin dakatar da shigar da kayan agaji zuwa cikin yankin wanda shi ma karya yarjejeniyar tsagaita wuta ce.