Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris

A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin.

A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin.

Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr.  

Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto ba su iya kai musu dauki.

A ranar 18 ga Maris, ne Isra’ila ta sake dawo da kai farmaki Gaza wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da ta fara aiki a watan Janairu.

Ana kuma tuhumar Isra’ila da laifin kisan kiyashi a gaban kotun kasa da kasa saboda yakin da ta yi da yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments