Rahotanni da suke fitowa daga Gaza sun ambaci cewa a tsakanin mutane 7 da su ka yi shahada da akwai karamin yaro.
Majiyar hukumar agaji ta Gaza ta ce karamin yaron ya yi shahada ne saboda bude masa wuta da sojojin mamaya su ka yi a yammacin birnin Gaza, sai kuma wani saurayi a kan titin Yafa a cikin wannan birni.
A can asibitin ‘al-Shifa’ dake cikin birnin Gaza an sanar da kai gawawwakin shahidai 4 da kuma wani adadi mai yawa na mutane da su ka jikkata. Sojojin mamaya sun yi amfani da jirgi maras matuki wajen kai harin akan falasdinawa a kusa da shatale-talen Haydar mai cunkoson mutane.
A wani labarin daga Gaza, da akwai falasdinawa fiye da 20,000 da yaki ya jikkata da kuma marasa lafiya da suke son a ba su izinin fita daga Gaza zuwa inda za su sami magani.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta rufe dukkanin kan iyakokin da marasa lafiyar za su iya samu su fita a kalla zuwa kasar Masar domin samun magani.
Adadin marasa lafiyar da su ka rasu a tsawon lokacin da suke jiran afitar da su zuwa samun magani sun kai1,344.
Gabanin a bar wani maras lafiya daya ya fita sai an bata masa lokaci mai tsawo na tambayoyi da kuma binciken kwakwaf.