Isra’ila ta ce ta saki Falasdinawa 200, ciki har da wasu kwamandojin kungiyar Hamas, a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cimma a Gaza.
Kungiyar kare hakkin fursunonin Falasdinu ta tabbatar da cewa daga cikin wadanda aka sako akwai Mohammed al-Tous, mai shekaru 69, wanda ya shafe kusan shekaru arba’in a tsare a hannun gwamnatin Isra’ila.
Musayar, wadda ita ce ta biyu tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, na zuwa ne bayan da Hamas ta saki wasu sojojin Isra’ila mata hudu a ranar Asabar.
Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta tabbatar da cewa a yanzu an kammala kashi na biyu na musayar fursunonin tsakanin Isra’ila da Hamas.
Isra’ila dai ta fitar da jerin sunayen fursunonin Falasdinawa sama da 700, wadanda za a saki a karkashin yarjejeniyar.
Fiye da fursunoni 230 ne ke zaman daurin rai da rai kuma za a tilasta musu gudun hijira na dindindin idan an sake su, ba wai dan su koma Falasdinu da zama ba saidai su nemi mafaka zuwa kasashen Aljeriya, Turkiyya ko Jordan a cewar kwamitin kula da harkokin fursunonin Falasdinawa dake da alaka da kungiyar kwantar ‘yancin palasdinawa ta PLO.