Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Adadin shahidai ya kai 39,445. An fitar da wannan lissafin ne a daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 299 da farawa.
Bugu da kari sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiyar Gaza, ta kuma ce; Adadin wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren HKI sun kai 91,073.
A wannan ranar ta 299 daga fara yakin na Gaza, HKI ta aikata wani kisan kiyashin inda ta kashe mutane 45,yayin da wasu 77 su ka jikkata.
Har ya zuwa dai ana cigaba da zakulo gawawwakin wasu shahidan da suke a karkashin kasa, sanadiyyar rushe gine-ginen da suke ciki a kansu da HKI ta yi.
A cikin zirin Gaza, HKI ta kai hare-hare a wuraren mabanbanta da su ka hada unguwar “Hayyut-tufah” da kuma gabashin birnin Gaza.
Da dama daga cikin wadanda su ka jikkata an kai su asibitin “Red-Corss” domin yi musu magani.